16 Yuni 2026 - 08:17
Source: ABNA24
Shekh Zakzaky: Al-Muharram Watan Da Aka Keta Hurumin Manzon Allah Da Iyalansa Tsarkaka Ta Hanyar Shekar Da Jinainensu

An kira shi Al-muharram ne saboda Allah ta'ala ya haramta shi. Wato haramun ne a yi yaƙi a cikinsa, yana da alfarma a wajen Allah. To, kuma har a jahiliyyah sun kasamce suna kulawa da alfarmar watanni masu alfarma.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: Jagora Allamah Sayyid Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) a wannan rana yayi bayani dangane da gabatowar watan Muharram da hurimin girmansa inda ya a cikin bayansa yak e cewa: To, wannan watan Al-muharram shi ne watan farko a shekara. An kira shi Al-muharram saboda Allah ta'ala ya haramta shi. Wato haramun ne a yi yaƙi a cikinsa, yana da alfarma a wajen Allah. To, kuma har a jahiliyyah sun kasamce suna kulawa da alfarmar watanni masu alfarma. A jahiliyyah ma an ce mutum yana iya ganin makashin Ubansa, don da su sun saba da fansa, amma in ya ganshi a haramin Makkah sai ya kyale shi, kuma in ya ganshi a wata mai alfarma sai ya ce; ka yi sa'a a Al-muharram na gamu da kai, da Safar ya kama da ka mutu. To, in kuma ya na dakon in Safar ya kama ya kashe shi, in bai ganshi ba har Safar ɗin ta zo, sa ya ce; sai ya gamu da shi a wani lokacin ba watan Alfarma ba, zai mutu. To, suna kiyaye wannan. Ba su kashe mutum a lokacin wata mai alfarma.

Don haka ne ma shi musamman Al-muharram ya zama sunansa ma kenan Al-muharram. Duk da yake ba shi kaɗai ne wata 'haram' ba. Ainihin Zalƙada da Zulhijjah ma haramomi ne. Rajab ma haram ne. Amma shi sai ya keɓanta da wannan sunan Al-muharram, saboda shi ne farkon shekara. Kuma shi musamman ma aka ce mishi wata mai alfarma, watan haramci.

To, kuma a wata mai kamar wannan ne aka keta wannan alfarman, a Musulunci. Alfarmar da ko jahiliyyah basu ketawa. Shi ne inda ainihin suka shekar da jinainan tsarkakan bayi na gidan Manzan Allah (S). Wannan kuma sai ya maida wannan lokaci namu na murna sai ya koma baƙin ciki. Sai ya zama lokaci ne da aka shekar da jinin Manzan Allah (S) a falalin Karbala. Duk iyalan gidansa gaba ɗaya aka rutsa da su, aka yanyanka su, aka karkashe, aka gutsittsira kawukansu, aka sossoke su a masu, aka tattara Matansu a matsayin ainihin ribar yaƙi. Aka kora su korawar bayi, aka bi gari-gari da su, ana bikin tariya, har aka kai su ga ainihin wani ja'iri, wanda ke rayawar yana mulki da sunan addini (addinin Musulunci). To, wannan sai ya zama wata ne na baƙin ciki.

Don haka tun kamawarsa ya kasamce ainihin a sunnar A'imma magabata, Abi Abdullah Imam Ja'afarus sadik, aka ce; ba a ganin ya yi dariya in Al-muharram ya kama, har sai bayan goma. Ya kan zama tun farawar watan ya kan zamo wata ne na musiba ɗin su, wata ne na jaje.

To, wannan jajen shi ne ma makasudin haɗuwarmu a nan. Daga yau ne wato ke nan zamu fara zaman jaje na jajanta wannan waƙi'a ta Karbala. Da tunatar da kawukanmu dangane da abin da ya faru, da kuma darussan da muke koyo dangane da wannan waƙi'a ɗin. Wanda wannan Alhamdulillah wannan ya rayu, da tun yana baƙo a wannan ɓangare namu ainihin, yanzu ya zama zaunannen abu. Yanzu ma har an kori cika-ciki, ya zama tsohon ya yi. Yanzun Al-muharram a matsayin watan jaje ya riga ya zauna daram. Kuma ainihin wannan al'amari ya riga ya zama jiki garemu. Kuma wannan haɓaka nasa, kodayake abin mamaki ne a wurinmu, amma har wala yau, hatta a inda aka san shi tunda wuri har wala yau haɓaka yake yi.

Al'amarin raya watan Al-muharram da kuma raya Arba'in ɗin Imam sai haɓaka yake yi. Wanda ya ke shiga sassa daban-daban na duniya, wanda yake har a inda aka san shi, alal misali; Karbala kanta, wanda birnin da ya kafu, masoya Abi Abdullahil Husain (a.s) suka haɗu suka kafa gari, suka zauna suka yi 'ajwarin' kayansa. Ya zama kuma mutane suna tuɗaɗa suna zuwa daidai wa'innan lokuta. Sai ya zama yanzu adadin mutane sai karuwa yake yi, sai karuwa yake yi. Ainihin wannan al'amari haɓɓaka yake yi sosai, wanda hatta a nan ma ya zama abin mamaki ballantana mu a nan ke nan. Mu a nan zamu iya cewa; abin mamaki ne. Sai mu ce; har a can ma ya zama abin mamaki don haɓakar da yake yi. Mu ko a nan da yake baƙo ne ma, kafin akai ga baƙuncin ya riga ya kau.

Wasallalhu Ala Muhammadin Wa'alihid Ɗahirin.

— Ɓangaren Jawabin Sheikh Zakzaky (H) a lokacin zaman farko na juyayin Ashura da yammacin ranar 1 ga watan Al-muharram 1436, a muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah, Zaria

— Sheikh Zakzaky's Library

01/Al-Muharram/1448. 16/06/2026

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha